Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Abba Sadiq kan zaben Faransa

Wallafawa ranar:

A Faransa, Benoit Hamon ya tsallake zagayen farko na zaben fidda gwani a matakin farko na jam’iyyar Socialist, in da yanzu haka zai fafata da tsohon Firaministan kasar Manuel Valls da yazo na biyu. Nasarar Benoit ta zo da mamaki lura da cewa bakon fuska ne a siyasar kasar, ko da dai ya taba rike mukamin ministan ilimi na gajeren lokaci. Tuni dai aka fara samun wasu daga cikin jam’iyyar Socialist da ke nuna goyon baya ga Benoit wanda ake gani zai doke Manuel Valls wajen zama dan takarar Socialist a zaben zaagaye na biyu. A zantarwarsa da Umaymah Sani Abdulmumin, Abba Sadiq, mazauni Faransa ya ce, babu shakka tauraron Benoit na haskawa tsakanin magoya bayan Jam’iyyar.

Benoit Hamon da Manuel Valls da ke neman kujerar takarar shugabancin Faransa karkashin jam'iyyar Socialist mai mulki
Benoit Hamon da Manuel Valls da ke neman kujerar takarar shugabancin Faransa karkashin jam'iyyar Socialist mai mulki ©JOEL SAGET / AFP
Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.