Bakonmu a Yau
Taron Paris : Farfesa Adamu Tanko na Jami’ar Bayero Kano
Wallafawa ranar:
Kunna - 04:04
A yau Litinin ake soma taron duniya na magance matsalar canjin yanayi a birnin Paris inda shugabanin kasashe 150 za su halarta. Taron na zuwa ne bayan an gudanar da zanga-zanga a sassan kasashen duniya domin kir aga shugabannin duniya su amince da yarjejeniyar rage fitar da gurbataccen iska. Game da taron Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Farfesa Adamu Tanko masanin kimiyar muhalli a Jami’ar Bayero da ke Kano, a Najeriya.