Ra'ayoyin Masu Saurare kan yajin aikin kungiyar kwadago ta Najeriya
Wallafawa ranar:
Kunna - 15:42
Kungiyoyin kwadago a Najeriya sun fara yajin aikin sai baba ta gana daga jiya Talata, matakin da suka ce sun dauke shi ne saboda nuna bacin rai dangane da dukan da aka yi wa shugabansu na kasa da kuma yadda gwamnati ta yi biris daga bukatunsu.
An dai fara yajin aiki ne duk da cewa kotu ta fitar da hukuncin da ke bayyana shi a matsayin wanda ya kauce wa ka’ida.
Shin ko wannan yajin aiki ke shafi yadda lamurra ke gudana a yankunanku?
Yaya kuke ganin cewa gwamnati da kungiyoyin kwadagon za su iya warware sabanin da ke tsakaninsu domin kawo karshen wannan yajin aiki?
Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu