Isa ga babban shafi
Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

Ra'ayoyin Masu Saurare kan sabon rikicin Mali

Wallafawa ranar:

A daidai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ke ci gaba da janye dakarunta na MINUSMA daga kasar Mali, bayanai na nuni da cewa fada ya sake barkewa tsakanin dakarun gwamnati da kungiyoyin ‘yan tawayen arewacin kasar da ke fafutukar kafa kasar Azawad. 

Wasu daga cikin 'yan tawayen Abzinawa a Mali
Wasu daga cikin 'yan tawayen Abzinawa a Mali © AP
Talla

 

Shi dai wannan fada ya fi yin kamari ne a zagayen birnin Kidal da ke karkashin mamayar ‘yan tawayen yau fiye da shekaru 10. 

Shin me za ku ce a game da wannan rikici da ya kunno kai a Mali yayin da a wani bangare kasar ke fama da kungiyoyin masu da’awar jihadi? 

Me za ku ce dangane da shirun kasashen duniya a daidai lokacin da kasar ke neman sake tsunduma cikin sabon yaki?

Ku latsa alamar sauti domin sauraren ra'ayoyi mabanbanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.