Kamfanin Dangote ya kaddamar da sabuwar matatar man fetur a Najeriya
Wallafawa ranar:
Kunna - 15:01
A yau Litinin ake sa ran shugaban Najeriya Mohd. Buhari ya kaddamar da sabuwar matatar man kamfanin Dangote da aka gina a birnin Lagos, wadda ake sa ran za ta rika tace gangar mai dubu 650 kowacce rana domin rage wahalar shigar da tacaccen mai cikin kasar.
Dangote ya ce ya kwashe shekaru sama da 20 yana bukatar sanya hannu a harkar man fetur da iskar gas, amma sai ya fuskanci kalubale daban-daban, wadanda daga bisani ya shawo kansu, abin da ya kai ga gudanar da wanann biki na yau.
Abin tambayar shine, ko samar da matatar man hakan zai taimaka wajen magance matsalar karancin fetur a kasar da ke Yammacin Afirka?
Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu