Isa ga babban shafi
Muhallinka Rayuwarka

Kamaru ta sako ruwan madatsar lagdo wanda ya janyo asarar kama daga rayuka da dukiyoyi

Wallafawa ranar:

A yau shirin zai bada hankali ne akan sakin ruwan madatsar ruwan lagdo da kamaru zata yi, wanda yanzu haka mazauna wasu yankuna da ruwan zai kwaranya ta cikin su a Najeriya ke cikin tashin hankali dangane da irin asarar kama daga ta rayuka har ya zuwa ta dukiyoyi.A karshe dai, gwamnatin Nigeria, ta tabbatar da cewa makwabciyarta Kamaru, ta sako ruwan da ke tumbatsa daga cikin madatsar ruwan Lagdo, lamarin da kan kasancewa babbar barazana ga dunbin al’ummomin Nigeria.

Yadda ambaliyar ruwa ta mamaye wasu sassan Jamhuriyar Nijar.
Yadda ambaliyar ruwa ta mamaye wasu sassan Jamhuriyar Nijar. © Tchadinfos.com
Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.