Isa ga babban shafi
Lafiya Jari ce

Cutar kazuwa ta addabi al'ummar wasu yankunan Jamhuriyar Nijar

Wallafawa ranar:

A wannan makon shirin Lafiya Jari ce ya mayar da hankali ne kan cutar kazuwa ko kuma Smallpox a turance, cutar da ke sahun cutuka masu matukar hadari da ke haddasa kuraje masu matukar kaikayi da mashasshara da kuma hana barci, wadda Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta sanar da kawar da ita daga ban kasa tun a shekarar 1980 amma kuma duk da haka ake ganin bullarta lokaci zuwa lokaci.

Cutar kazuwa wadda ake alakantawa da kazanta a baya-bayan nan an samu barkewarta a wasu kauyukan Jihar Maradi ta jamhuriyyar Nijar.
Cutar kazuwa wadda ake alakantawa da kazanta a baya-bayan nan an samu barkewarta a wasu kauyukan Jihar Maradi ta jamhuriyyar Nijar. REUTERS - STRINGER
Talla

Cutar ta kazuwa wadda ake alakantawa da kazanta a baya-bayan nan ne aka samu barkewarta a wasu kauyukan Jihar Maradi ta Jamhuriyyar Nijar, inda masana ke cewa zuwa yanzu akwai fiye da mutum dubu 3 da suka harbu, kuma kaso mai yawa na Almajirai da magidanta sai kuma kananan yara musamman a kauyukan Surori zuwa Tsibiri da kuma garin Udal, wanda ke matsayin karon farko da aka ga bullar cutar bayan shafe tsawon shekaru ba tare da jin duriyarta ba.

Ku latsa alamar sauti don sauraron shirin tare da Azima Bashir Aminu....

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.