Isa ga babban shafi
Lafiya Jari ce

Gangamin gwajin cutukan sankarar mama da kansar bakin mahaifa a Nijar

Wallafawa ranar:

Shirin Lafiya Jari ce a wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan wani gangamin gwajin cutar kansar mama da ta bakin mahaifa da mahukuntan Nijar suka gudanar a jihar Maradi a wani yunkuri na lalubo masu cutar tare da yi musu magani.

Sankarar mama na sahun cutukan kansa mafiya saurin kisa ga Mata.
Sankarar mama na sahun cutukan kansa mafiya saurin kisa ga Mata. ©AFP
Talla

Wannan mataki na gwajin cutukan kansar biyu na da nasaba da sabbin alkaluman da ke nuna karuwar masu dauke da cutar a sassan Faransa.

Tuni dai Mata suka yi dafifi wajen yin wannan gwaji wanda aka tattara kwararrun likitoci da ke aikin wayar da kai tare da bayar da shawarwari kan yadda mata za su kula da lafiyarsu kasancewar cutukan kansar guda biyu a matsayin mafiya saurin kisa a tsakanin al'umma musamman a kasashe masu tasowa.

Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.