Dandalin Fasahar Fina-finai
Fili ne na musamman kan Fina-finai ta hanyar tattauna da masu ruwa da tsaki a wannan fanni a duniya, Tare da wayar wa ma su sauraro kai da kara masu basira dangane da hikimar da Allah ya bai wa wasu ta fanin shirya fim ko tsara wasan kwaikwayo. Wanda ke zo maku a duk ranar Asabar da safe, tare da maimaici a ranar Lahadi da yamma.
Ci gaban karatuSaurari kashin karshe
Daukacin kashi-kashi
-
Mutane na yi wa fim kallon hadarin kaji don ba su ke yi ba - Isa Bello Ja
A cikin shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' Hauwa kabir ta kawo abubuwa da dama a bangaren fina-finai, inda ta duba yadda yanzu masana'antar Kannywood ke gogayya da takwararta tav kudancin Najeriya. Ta kuma tattauna da shugaban jaruman Kannywood, Alhassan Kwale wanda ya ce Umma Shehu da Sadiya Haruna ba 'yan Kannywood bane.29/08/202120:41 -
Tattaunawa da Yaya Dankwambo na shirin gidan Badamasi
Shirin Dandalin Fasahar Fina-Finai na wannan makon tare da Hauwa Kabeer ya tattauna da Muhammadu Nura Yakubu da a yanzu aka fi sani da sunan Yaya Dankwambo na shirin fim din Gidan Badamasi.22/08/202120:00 -
Tattaunawa da Tijjani Asase (Damisa) kan masana'antar Kannywood
Shirin Dandalin Fasahar Fina Finai ya tattauna da Tijjani Asase da aka fi sani da Damisa kan lamurran da suka shafi masana'antar Kannywood.15/08/202120:00 -
Ana shirin ci gaban fim din Hausa na 'Malam Zalimu'
A cikin shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' Hauwa Kabir ta duba tattauna da Ado Ahmed Gidan Dabino a game da ci gaban shirin fim din Malam Zalimu. Bayan nan ta leka Nollywood ta kudancin Najeriya, inda ta kawo ta'aziyar rasuwar shahararren mawaki, Sound Sultan.25/07/202120:00 -
Masu shirya Fina finan Hausa sun koma cin moriyar Youtube
A cikin shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' Hauwa Kabir ta yi dubi da batun kasuwanci a masana'antar Kannywood, tare da duba yadda masu shirya fim din suka koma intanet, ta wajen cin moriyar dandalin Youtube, inda suke dora ayyukansu a kai.18/07/202120:00 -
Dandalin Fasahar Fina-Finai: Ta'aziyyar jaruma Zainab Booth
A cikin shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' na wannan makon, Hauwa Kabir ta kawo ta'aziyyar jarumar Kannywood da Allah ya wa rasuwa a makon da ya gabata,inda ta tattauna da abokan aikinta na Kannywood. Shirin ya kuma leka Nollywood da Bollywood.11/07/202120:00 -
Jarumai mata na fuskantar kalubale daga masu kallo a kafafen sada zumunta
Shirin Dandalin Fasahar Fina-Finai na wannan makon ya tattauna kan yadda Jarumai musamman mata a musamman a masana'antar shirya fina-finai ta Kannywood ke fuskantar cin zarafi daga masu kallo a kafafen sada zumunta na zamani.27/06/202120:00 -
Rayuwar mawaka a Duniyar yan fim a Najeriya
Mawaka fina-finai a Najeriya na rayuwa ba tareda sun ci moriyar aikin da suke yi ba,banda haka Hawa ta samu tattaunawa da Haro mawakin hausa a Kaduna dake Najeriya.A cikin shirin Duniyar Fina-finai tareda Hawa Kabir,ta samu tattaunwa da wasu dake ruwa da tsaki a Duniyar Fina-finai a Najeriya.Hawa Kabir ta samu20/06/202120:00 -
Tattaunawa da Isa Bello Ja da kuma rikicin fitattun mawaka mata a Nollywood
Shirin Dandalin Fasahar Fina-finai na wannan makon tare da Hauwa Kabir, ya tattauna da wasu tsoffin 'yan wasan Kannywood cikinsu har da Isa Bello Ja. Kana shirin ya kuma tattaunawa dangane da cacar baki da fitattun mawakan Kudancin Najeriya mata biyu sukayi da ya karade shafukan sada zumunta.13/06/202120:00 -
Sai babba ya watsar da girmansa ake rena shi a Kannywood- Isa Bello Ja
A cikin shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai na wannan makon, Hauwa Kabir ta tattauna da wasu fitattun jaruman Kannywood, ta kuma leka Nollywood, na kudancin Najeriya don ganin wainar da ake toyawa.06/06/202120:00 -
Yadda fim mai dogon zango ke tasiri a Kannywood
A cikin shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' na wannan makon, hauwa Kabir ta tattauna da wasu jaruman fim din nan mai dogo zango da ake yi a tashar arewa 24, wato 'Kwana Casa'in', inda suka yi bayani a kan yadda irin nau'in fim din ke samun karbuwa a Kannywood.23/05/202120:00 -
Dandalin Fasahar Fina-finai ya yi tattaki zuwa Katsina, Nollywood
Shirin Dandalin Fasahar Fina-finai ya yi tattaki zuwa Katsina don tattaunawa da mawaki, Boda a kan wakar gamayya ta Ramadan, kana ya leka masana'antar frina-finai ta kudancin Najeriya, Nollywood don jin wainar da ake toyawa danagane da zargin da ake wa wani jarumin masana'antar na cin zarafin wata karamar yarinya.09/05/202120:00 -
Mawakan Hausa sun yi hadaka a wakokin azumin Ramadan
A cikin shirin 'Dandalin Fasahar Fina - Fiinai, Hausa Kabir ta yi hira da mawakin Hausa, Abba Don , wanda ya jagoranci hadakar mawaka wajen raira wakar azumin wata Ramadan. A yi sauraro lafiya.02/05/202120:00 -
Kalubalen da ake fuskanta na rashin fahimta tsakanin taurari da masu shirya fim
Shirin Dandalin Fasahar Fina-finai na wannan makon ya cika da tattaunawa da masu ruwa da tsaki akan matsalolin dake kunno kai tsakanin masu shirya fina-finai da kuma taurari.04/04/202120:00 -
Dandalin Fasahar Fina-Finai: Tattaunawa da Tahir Fagge
A cikin wannan shiri na 'Dandalin fasahar Fina-Finai', Hauwa Kabir ta tattauna da babban tauraro a masana'antar Kannywood ta fina-finan Hausa Alhaji Tahir Fagge, inda ya yi bayani a ka gwagwarmayar rayuwa da irin kalubalen da suka addabi sana'arsa. Hauwa ta kuma duba masana'antar fina-finan Yarabawa a kudancin Najeriya.28/03/202120:00
Dandalin Fasahar Fina-finai
Fili ne na musamman kan Fina-finai ta hanyar tattauna da masu ruwa da tsaki a wannan fanni a duniya, Tare da wayar wa ma su sauraro kai da kara masu basira dangane da hikimar da Allah ya bai wa wasu ta fanin shirya fim ko tsara wasan kwaikwayo. Wanda ke zo maku a duk ranar Asabar da safe, tare da maimaici a ranar Lahadi da yamma.