Kwanaki 26 bayan barkewar yakin dake ci gaba da gudana ba tare da kaukautawa ba tsakanin Isra’ila da kungiyar Hamas, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane kusan dubu 10, ana fargabar yakin na iya fadada musamman ganin yadda kungiyoyi irin su Hezbollah da Houthi suka fara harba makamai a kan Israila.
Masana na bayyana cewar ganin yadda Majalisar Dinkin Duniya kuma kasashen dake da karfin fada aji suka gaza samar da Shirin tsagaita wuta, yakin na iya daukan dogon lokaci.
A kan haka, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dakta Bashir Nuhu Mabai na Jami’ar Dutsinma da ke Katsinan Najeriya.
Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu