Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Janar Saleh Maina kan rikicin kasar Sudan

Wallafawa ranar:

Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar kasashen Afirka na ta kokarin samo hanyar yin sulhu domin kawo karshen rikicin da ake ci gaba da yi a kasar Sudan Wanda ya lakume rayukan mutane sama da 500. 

Janar Saleh Maina
Janar Saleh Maina AFP via Getty Images - PIUS UTOMI EKPEI
Talla

Fadan da ake gwabzawa a kasar Sudan ya hada da dakarun da ke biyayya ga babban hafsan sojin kasar Abdel Fattah al-Burhan da na tsohon mataimakinsa Mohamed Hamdan Daglo, wanda ke jagorantar rundunar kai daukin gaggawa ta musamman.

Wannan lamari dai, ya tayar da hankulan jama'a a wani abu da ake ganin yakin basasa ne, daidai lokacin da al’ummar Sudan ke kokarin farfado da tsarin mulki na farar hula ta dimokuradiyya, bayan shekaru da dama suna karkashin mulkin soja.

Kan wannan takaddama ne, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da tsohon kwamandan runduna ta 3 ta sojin Najeriya, Janar Saleh Maina.

Shiga alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.