Dauda Lawal Dare kan makomar jihar Zamfara a hannun sabuwar gwamnati
Wallafawa ranar:
Kunna - 04:42
Zababben gwamnan jihar Zamfara dake Najeriya, Dakta Dauda Lawal Dare yace ba zai waiwayi shirin sulhun da gwamnatin jihar ta kulla da ‘yan bindiga ba, saboda yadda ya kasa samar da maslaha ga jama’ar jihar.
Wannan na zuwa ne yayin da jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Najeriya, ke fuskantar kalubalen hare-haren 'yan bindiga, inda suke kai farmaki kan mutane, musamman mazauna karkara.
A tattaunawarsu da Bashir Ibrahim Idris, Dakta Lawal yace aniyarsa itace na ganin ya samar da dawamammen zaman lafiyar da jama’a za su koma garuruwansu domin gudanar da harkokinsu na yau da kullum.
Shiga alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu