Dr Mustapha Zakari masanin muhalli dangane da girgizar kasa a Turkiya da Syria
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:39
Adadin wadanda suka mutu sakamakon girgizar kasar da ta afkawa Turkiya da Syria ya haura mutane dubu 11, yayin da jami’an agaji ke cigaba da aikin ceto wadanda baraguzan gine-gine suka danne.Yanzu haka dai akwai fargabar yawan wadanda suka mutu a girgizar kasar ka iya karuwa da adadi mai yawa, inda jami’an hukumar lafiya ta duniya suka yi hasashen yawan mamatan ka iya kaiwa mutane dubu 20.
Kan wannan iftila’i Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dakta Mustapha Zakari Karkarna masanin Muhalli da kimiyyar hallitun da suke zagaye da shi a Jami'ar Bayero, kuma tsohon Kwamishinan Muhallin a Jihar Jigawa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu