Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Shu'aibu Liman kan matakin gwamnatin Zamfara na rufe wasu kafofin yada labarai

Wallafawa ranar:

Hukumar kula da kafofin yada labaran Najeriya tare da Kungiyar 'yan jarida ta kasar da kuma kungiyar kafofin yada labaran Rediyo da Talabijin sun yi Allah wadai da matakin da gwamnatin jihar Zamfara ta dauka na rufe wasu kafofin yada labarai guda 5 saboda abinda ta kira dauko rahotan taron siyasa.

Gwamnan jihar Zamfara a Najeriya Bello Matawalle, a cikin ofishinsa dake jihar
Gwamnan jihar Zamfara a Najeriya Bello Matawalle, a cikin ofishinsa dake jihar © Governor Matawalle
Talla

Hukumar NBC ta hannun shugaban ta Balarabe Shehu Ilela ta zargi gwamnatin Zamfara da wuce makadi da rawa, yayin da kungiyar 'yan Jarida ta bayyana matakin a matsayin kama karya.

Dangane da wannan al’amari, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Sakataren Kungiyar 'yan Jarida na kasar Shu'aibu Liman.

Shiga alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.