Taron Ministocin muhalli na kasashen Afirka tare da kungiyoyin kare muhalli da aka kammala a Kinshasa, ya sake jaddada bukatar karin kudade daga manyan kasashen duniya domin rage radadin gurbata muhallin da suke yi.
Kudaden sun kunshi na taimako da kuma diyya saboda illar da kasashen Afirkan ke fuskanta.
Dangane da wannan matsayi, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Malam Sani Ayouba, na kungiyar Sakai ta matasan Afirka daga Jamhuriyar Nijar, na daya daga cikin wadanda suka halarci taron.
Latsa alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu