Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Dakta Peter Ajohnson game da kai dauki ga Arewa maso Yammacin Najeriya

Wallafawa ranar:

Kungiyar Agaji ta Medicins Sans Frontier ta bukaci kungiyoyin agaji da su kai dauki ga mutanen yankin Arewa maso Yammacin Najeriya dake fama da dimbin matsaloli sakamakon tashe tashen hankulan da ake samu a yankin.

Jami’an hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa da kasa ICRC, yayin raba abinci ga ‚yan gudun hijira da tashe-tashen hankula suka raba da muhallansu a garin Maiduguri.
Jami’an hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa da kasa ICRC, yayin raba abinci ga ‚yan gudun hijira da tashe-tashen hankula suka raba da muhallansu a garin Maiduguri. © ICRC
Talla

 

Darakatar kungiyar a Najeriya, Dr Simba Tirima, tace tun daga farkon wannan shekarar, jami’an su sun ga tarin kananan yaran dake fama da matsalar karancin abinci mai gina jiki wadanda ta danganta da tashe tashen hankula da sauyin yanayi da kuma tsadar abinci, yayin da suka taimakawa kusan dubu 100 a Cibiyoyin su 34, tare da kwantar da kusan dubu 17 a asibiti a Jihohin Kano da Zamfara da Katsina da Sokoto da kuma Kebbi.

Dangane da wannan matsala, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dakta Peter Ajohnson, jami’i a kungiyar.

Latsa alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.