Ambasada Ibrahim Kazaure kan shirin yakin neman zabe a Najeriya
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:41
Yayin da Jam’iyyun siyasar Najeriya ke shirin kaddamar da yakin neman zaben da zai gudana a shekara mai zuwa, hukumar zaben kasar ta gana da shugabannin addinai, domin janyo hankalin su, wajen ganin sun fadakar da jama’a kan yadda za a kaucewa tashe tashen hankula.
Wadannan bangarori sun bukaci shugabannin Jam‘iyyu da 'yan takara da su ja kunnen magoya bayan su, ta yadda za su kaucewa kalaman batanci ko kuma tunzura jama'a.
Dangane da wannan matsayi, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Ambasada Ibrahim Kazaure, tsohon ministan ayyuka na musamman a Najeriya.
Latsa alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu