Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Abubakar Sadiq kan rushewar gine-gine da ya yi ajalin mutum 86 a Najeriya

Wallafawa ranar:

Hukumomin Najeriya sun sanar da cewar mutane 86 suka mutu sakamakon rushewar gine gine a biranen kasar cikin watanni 10 da suka gabata, abinda ke nuna karuwar matsalar gini da kuma rashin ingancin sa.

Wani bene da ya zube a jihar Legas kenan
Wani bene da ya zube a jihar Legas kenan REUTERS - NNEKA CHILE
Talla

Daga cikin wannan adadi harda bene mai hawa 21 da ya rushe a Lagos, wanda kwararru ke sanya ido wajen gina shi.

Wannan matsala ta sanya kwamishinan kula da gine gine na jihar Lagos, Jide Idris aje mukaminsa.

Dangane da wannan matsala mai tada hankali, Bashir Ibrahim ya tattauna da Malam Idris Abubakar Sadiq, mataimakin shugaba na 3 na kungiyar masu kula da gine gine a Najeriya.

Latsa alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.