Aliyu Dawobe kan ranar bikin tunawa da mutanen da suka bata a duniya
Wallafawa ranar:
Kunna - 04:01
Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar 31 ga watan Agustan kowacce shekara a matsayin ranar da ake mayar da hankali akan mutanen da suka bata, inda kungiyar agaji ta ICRC tace a nahiyar Afirka kawai ana da mutane dubu 64 da suka bata.
Alkaluman kungiyar sun bayyana cewar a Najeriya kawai akwai mutane sama da dubu 25 da suka bata, kuma kusan dubu 14 daga cikin su yara ne kanana.
Dangane da bikin irin wannan rana, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Daraktan yada labaran kungiyar ICRC a Najeriya, Aliyu Dawobe.
Latsa alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu