Dakta Muhammad Babayo kan albashin malaman jami'o'i a Najeriya
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:42
Gwamnatin Najeriya tace babu gudu babu ja da baya dangane da shirin ta na kin biyan malaman jami’oin dake yajin aiki albashin su na watanni 5 da suka gabata, saboda kin koyar da yara a makarantu.
Ministan ilimi Adamu Adamu yace bangarorin biyu sun cimma yarjejeniya akan batutuwa da dama amma banda batun biyan albashin.
Dangane da halin da ake ciki akan yajin aikin, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dakta Muhammad Adamu Babayo, dan majalisar zartarwar kungiyar malaman a kasar .
Latsa alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu