Nastura Ashir Shariff kan cin zarafin 'yan arewacin Najeriya a kudancin kasar
Wallafawa ranar:
Kunna - 04:05
Kungiyoyin matasa daga yankin arewacin Najeriya sun bayyana damuwa akan yadda wasu jihohin kudancin kasar ke tare matafiya ci rani suna cin zarafin su a yankin kudu.
Wannan korafi ya biyo bayan tare wasu motoci dauke da yan arewacin Najeriya akalla 350 da kungiyar tsaron Amotekun tayi a Jihar Ondo, inda aka bayyana su a matsayin masu mamaya.
Matasan yan ci rani sun fito ne daga jihohi irin su Kano da katsina da kaduna da Jigawa domin zuwa kudu yin sana’a.
Dangane da wannan matsala, Bashir Ibrahim Idris ya zanta da shugaban gamayyara kungiyoyin matasan arewa, Nastura Ashir Shariff.
Latsa alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu