Bakonmu a Yau
Injiniya Muhammad Tukur kan matsalar sufurin jiragen sama a Najeriya
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:33
Rahotanni daga Najeriya na nuna cewar harkar sufurin jiragen sama a kasar na fuskatar barazanar durkushewa inda yanzu haka jiragen fasinja 38 kacal ke aiki daga cikin sama da 90. Tuni wannan matsalar ta haifar da matsalolin zirga zirga da kuma tsadar tikitin tafiye tafiye a cikin gida tare da fuskantar jinkiri wajen samun jiragen tafiya. Dangane da wannan matsala, Bashir Ibrahim Idris ya zanta Injiniya Muhammad Tukur, masani a bangaren sufurin jiragen saman, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.