Daruruwan al’ummar Hausawa ne suka gudanar da zanga-zanga a birane daban-daban na kasar Sudan, inda suke neman a yi musu adalci bayan barkewar rikicin kabilanci da ya yi sanadiyar kashe musu mutane da dama a yakin kogin Nilu.
Akalla mutane 79 suka mutu, wasu 199 suka samu raunuka bayan barkewar rikicin tsakanin Hausawa da 'yan kabilar Barti Larabawa a ranar Litinin din makon jiya.
Malam Umar Hamza Abdullaye na daga cikin wadanda suka halarci zanga-zangar kuma ya yi wa Bashir Ibrahim Idris karin bayani.
Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirarsu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu