Bayan shafe sheraka da shekaru suna kaiwa jama’a hare-haren ta’addanci da garkuwa da mutane, a yanzu dai a iya cewa sojojin Najeriya sun fara galaba kan ‘yan bindiga da suka addabi jihar Zamfara. Wannan nasara dai na zuwa ne bayan da hukumomi a jihar suka bada umarnin rufe wasu kasuwanni da hana sayar da man fetur a kan tituna, kafin daga bisani a katse layukan waya.
Shin ko kaste layukan wayar ta yi wani tasiri wajen yaki da ‘yan bindigar?
Rukayya Abba Kabara ta tattauna da Dr. Sulaiman Shu’aibu Shinkafi, daya daga cikin dattawan jihar Zamfara mai fama da tashin hankali.
Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakkiyar hirarsu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu