Faruk Adamu Aliyu kan yadda manoma suka koma gona a Najeriya
Wallafawa ranar:
Kunna - 04:09
Yayin da gwamnatin Najeriya ke ta kiraye-kirayen cewar mutane su koma gona domin samar da abinci, yanzu haka wasu al’ummar kasar sun rungumi shirin, kuma sun koma aikin gonar gadan-gadan.
Daga cikin wadanda suka amsa kiran, har da tsohon shugaban marasa rinjaye a Majalisar dokokin Najeriya, Hon Faruk Adamu Aliyu wanda ya samar da wata katafariyar gonar da ake noma abinci da kiwon dabbobi da kuma sarrafa takin zamani.
Bashir Ibrahim Idris ya ziyarci gonar, bayan an zagaya da shi, ya gane wa idanunsa yadda take, sannan ya tattauna da shi.
Ku latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakkiyar hirarsu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu