Shirin Al'adunmu na Gado na wannan makon ya yada zango ne a dutsen Koma da ke jihar Adamawar Najeriya, inda ya tarar da mutanen Kabilar Koma da ke gudanar da tsantsar rayuwar gargajiya irin wadda aka yi ta dubban shekaru da suka gabata.
Har yanzu mutanen na Kabilar Koma na amfani da ganye ne wajen rufe tsaraicinsu, sannan kuma suna da irin gishirinsu na girki da suke miya da shi irin nasu. Kazalika suna amfani da wani irin salo wajen kunna wutar kirki ba tare da ashana ta zamani ba.
Kuna iya kallon bidiyon yadda wadannan mutane ke rayuwa a shafinmu na Facebook da Youtube.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu