Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Tattaunawa da Dr Sani Abdullahi Shinkafi kan bukatar kungiyarsu na sake bincikar mutanen da hukumomi suka kama a Zamfara kan zargin ganawa da 'yan bindiga

Wallafawa ranar:

Wata kungiya da ke fatan samar da zaman lafiya da ci gaba a tarayyar Najeriya ta nemi a gudar da bincike kan mutanen da ‘yan sanda suka kama a jihar Zamfara cikin kwanakin da suka gabata, bisa zargin cewa sun yi ganawar sirri da wasu tubabbin ‘yan bindiga da suka yi kaurin suna wajen aikata kisa da kuma yin garkuwa da mutane a jihar.To sai dai kungiyar ta yi zargin cewa sakamakon matsin lamba da kuma tsoma bakin wasu manyan ‘yan siyasa daga Abuja, ala dole jami’an tsaro suka saki mutanen 16.Dr Sani Abdullahi Shinkafi shi ne shugaban kungiyar, ga kuma abin da ya shaida wa Abdoulkarim Ibrahim Shikal.

A makon da ya gabata ne gwamnatin Jihar Zamfaran ta sanar da kame na hannun daman tsohon Gwamnan jihar kan wannan zargi.
A makon da ya gabata ne gwamnatin Jihar Zamfaran ta sanar da kame na hannun daman tsohon Gwamnan jihar kan wannan zargi. REUTERS/Goran Tomasevic/File Photo
Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.