Isa ga babban shafi
Siyasa

Zaben raba gardamar sabon kundin tsarin Mulki a Nijar

Wallafawa ranar:

Zaben raba gardamar da Al’ummar kasar jamhuriyar Nijar suka gudanar a ranar 31 ga watan Oktoba 2010, kan sabon kundin tsarin Mulkin Jamhuriya ta bakwai, ya samu amincewar kashi 52,18% na yawan kuru’un da aka kada.  

'Yan takarar Shugaban kasar Nijar guda biyar
'Yan takarar Shugaban kasar Nijar guda biyar RFI Hausa
Talla

Samun nasarar gudanar da wannan zaben da ya kasance na farko daga cikin jerin zabubbukan da aka shirya yi, domin sake maida kasar kan turbar demokradiya, ya fara sanyaya zukatan yan siyasar kasar, kan samun tabbacin cewa, mahukumtan mulkin sojan kasar, sun fara cika Alkawulan da suka dauka, wajen sake maida mulki ga hannun fararar hular da suka kwata, a karakashin Mulkin Shugaba Tanja Mamadu, a ranar 18 ga watan Fabarairun 2010.

An Bada Sakamakon Zaben Raba Gardama a Nijar
00:18

Abdurahman Gusman, shine shugaban hukumar zaben

To’ a cikin wannan shiri, mun tattauna da shugaban Jam’iyar PNDS Tarayyar, Mahamadu Isufu, da shugaban Jam’iyar Lumana, Hama Amadu, tare da mataimakinsa Mahamadu Salisu Habi, sai kuma sakataren yada labaran jam’iyar MNSD Nassara, da sojoji suka kifar da gwamnatinta, Abdurra’uf Sidi. A yi sausare Lafiya !
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.