Isa ga babban shafi

Zaftarewar kasa ta kashe almajirai guda 8 a Birnin Kebbi

Najeriya – Akalla yara almajirai guda 8 zabtarewar kasa ta kashe a Birnin Kebbi dake Najeriya lokacin da suka je aikin saran kasar da za'ayi amfani da ita domin aikin gini.

Gwamnan Jihar Kebbi, Dr Nasir Idris
Gwamnan Jihar Kebbi, Dr Nasir Idris © Daily Trust
Talla

Rahotanni sun ce an samu wannan iftila'in ne yau asabar da safe lokacin da almajiran suke je gudanar da wannan aiki domin yin gini.

Kantoman karamar hukumar Birnin Kebbi Mohammed Dahiru Ambursa ya tabbatar mana da aukuwar lamarin da kuma mutuwar wadannan almajirai guda 8 wadanda suka fito daga sassan jihar domin koyon karatun Alkur'ani a birnin.

Ambursa ya ce da misalin karfe 2 na ranar yau ake saran yiwa wadannan yara jana'iza, yayin da wasu guda 3 kuma ke can asibiti ana kula da lafiyar su saboda raunin da suka samu.

Kantoma yace tuni suka bada umarnin killace wurin da aka samu hadarin da kuma shelar hana aiki a wurin.

Ambursa ya kuma jajantawa iyayen wadannan yara da suka rasa rayukansu, tare da bai wa uwayen kasa umarnin shelar hana ginan kasa a wannan wuri.

Sanya yara almajirai aikin karfi domin samun abinda za su ci ba sabon abu bane a sassan arewacin Najeriya, abinda ya sa kungiyoyi da dama ke kiran sake fasalin koyon karatun Alkur'ani ta yadda iyaye zasu dinga daukar nauyin ciyar da 'yayan su, yayin da suke daukar karatun a gaban malamai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.