Isa ga babban shafi

Ƴan bindiga sun tilasta mutane kusan 290 barin muhallansu a Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna da ke Najeriya ta ce hare-haren ƴan bindiga sun tilasta wa mutane dubu 289 da 375 daga kauyuka 551 na kananan hukumomin jihar 12 barin matsugunansu.

'Yan bindiga sun addabi wasu yankuna a jihohin Najeriya.
'Yan bindiga sun addabi wasu yankuna a jihohin Najeriya. © Leadership
Talla

Babban Daraktan Hukumar kai daukin gaggawa ta jihar Kaduna Usman Mazadu ke sanar wannan alkaluma yayin da yake kaddamar da aikin rarraba kayayyakin tallfin abinci a Maraban kajuru jiya Laraba.

A cewar Mr Mazadu, a Karamar Hukumar Chikun kadai, mutane dubu 26 da 345 daga kauyuka 134 ne suka tsere daga matsugunansu saboda tsanantar hare-haren ƴan bindigar sai kuma wasu dubu 70 da 893 daga kauyuka 84 na Karamar Hukumar Birnin Gwari.

A cewar shugaban Hukumar Agajin ta Kaduna abin takaici ne yadda hare-haren ƴan bindigar ke ci gaba da dankwafe fatan iyalai da dama ciki har da batutuwa masu alaka da ilimi, lafiya da kuma ayyuka baya ga jin dadin rayuwa.

Hukumar  Agajin ta Kaduna ta ce matakin karuwar mutanen da rikici ya raba da matsugunansu, ya tilasta wa gwamnan jihar Uba Sani ware Naira biliyan 11 da rabi don tallafa musu ga kayakin rage radadin rayuwa.

Hare-haren ƴan bindiga na ci gaba da tsananta a sassan jihar Kaduna, inda batagarin kan sace mutane don neman fansa ko kuma kisan ba gaira-babu-dalili, lamarin da ya ke sanya mutane hijira daga kauyuka zuwa birni.

Kwanan nan ƴan bindigar suka sace dalibai kafin a ceto su

Gwamnan jihar Kaduna da ke Najeriya, Sanata Uba Sani ya mika daliban makarantar Kuriga ga iyayensu bayan sun shafe kimanin sa'o'i 48 a hannun gwamnati ana kula da lafiyarsu sakamakon wahalar da suka sha a hannun 'yan bindigar da suka yi garkuwa da su.

Gwamnan ne ya sanar da mika daliban a shafinsa na Facebook a wannan Alhamis, yana mai cewa, ya mika daliban cikin sosuwar zuciya.

Gwamnan Kaduna Uba Sani a yayin mika daliban makarantyar Kuriga ga iyayensu.
Gwamnan Kaduna Uba Sani a yayin mika daliban makarantyar Kuriga ga iyayensu. © Kaduna State Governor

Gwamnan ya tabbatar cewa, sai da aka tabbatar da cikakkiyar lafiyar jiki da ta kwakwaluwar daliban kafin yanke shawarar mika su ga iyayensu da suka dade cikin zumudin haduwa da yaran nasu.

Gwamnan ya kara da cewa, daliban wadanda ya dauka a matsayin 'ya'yansa na ciki sun yi masa alkawarin cewa, za su mance da mummunar jarrabawar da ta same su tare da mayar da hankali kan karatunsu.

Domin nuna godiya kan jajircewar da yaran suka nuna, da kuma tsayin-dakarsu kan cimma burinsu na neman ilimi duk da mummunan ibtila'in da ya same su, gidauniyar Uba Sani za ta dauki nauyin karatunsu har zuwa matakin makarantar gaba da sakandare.

A bangare guda, gwamnan na Kaduna ya yi alkawarin cewa, zai biya diyya da iyalan Malam Abubakar wanda ya rasa ransa a hannun 'yan bindigar da suka kaddamar da farmaki kan makarantar ta Kuriga, inda gwamnan ya ce, zai bai wa iyalan nasa diyyar naira miliyan 10.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.