Isa ga babban shafi

An kama mutane takwas bisa zargin su da kisan wasu ‘yan sanda a Jihar Deltan Najeriya

Wasu matane 8 sun shiga ragayar 'yansandan Najeriya a jihar Adelta akan aikakata laifin kisan wasu 'yan sandan kasar da ke bakin aikinsu.  

'Yan sandan Najeriya da aka baza a wani yankin kasar.21/10/21
'Yan sandan Najeriya da aka baza a wani yankin kasar.21/10/21 REUTERS - AFOLABI SOTUNDE
Talla

 

Jami’an tsaro a Najeriya sun cafke mutane takwas bisa zargin su da kashe ‘yan sanda takwas a garin Ughelli dake jihar Delta, kamar yadda kakakin Rundunar ACP Olumuyiwa Adejobi ya bayyana.

Ya kara da cewa a yayin wani bincike ne aka yiwa ‘yan sandan kwantan bauna inda aka kasha shida daga ciki sauran kuma suka tsere.

Adejobi ya ce Rundunar ta yi nasarar cafke mutane biyar da ake zargi da aikata laifin jim-kadan da aukuwar lamarin, yayin da sauran mutane ukun sai da aka tsaurara bincike aka yi kamo su a wurare mabanbanta.

Ya kara tabbatar da cewa Rundunar na aiki tukuru ba dare ba rana don ganin ta cafke tare da hukunta wadanda ke da hannu wurin aikata wannan laifi dama makamancinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.