Isa ga babban shafi

Tinubu ya haramtawa ministocinsa balaguro zuwa ketare na watanni 3

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya haramtawa ministocinsa tafiye-tafiye har na tsawon watannin 3 a wani yunkuri na rage kudaden da ake kashewa yayin bulaguron na su zuwa kasashen ketare.

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu.
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu. © Bola Ahmed Tinubu twitter
Talla

Wata wasikar shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Femi Gbajabiamila mai dauke da kwanan watan 12 ga watan Maris 2024 wadda kuma sakataren gwamnatin kasae George Akume ya gabatar da ma’aikatun ta bayyana cewa haramcin tafiye-tafiyen zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Aprilun shekarar nan.

Tun a watan Janairun da ya gabata ne dai shugaban Najeriyar Bola Tinubu ya gabatar da wata doka da ta bukaci rage yawan mutanen da za su rika yi masa rakiya zuwa kasashen ketare yayin bulaguro a wani yunkuri na zaftare kudaden da ake kashewa.

Karkashin dokar dai shugaban ya bukaci rakiyar mutane 25 kadai a tafiye-tafiye na cikin gida sai kuma rakiyar mutane 20 yayin bulaguro zuwa ketare.

Sai dai duk da hakan shugaban ya gamu da kakkausar suka bayan tawagar mutane 590 sun masa rakiya zuwa birnin Dubai na hadaddiyar Daular Larabawa yayin taron yanayi na COP28 ko da ya ke gwamnatin ta ce mutane 422 kadai ta dauki nauyin balaguron na su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.