Isa ga babban shafi
labarin aminiya

An gurfanar da Amal kan zargin bai wa dan sanda cin hanci

An gurfanar da fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood a gaban kotun Majistare da ke Gyadi-Gyadi a Jihar Kano, kan zargin yunkurin bai wa wani jami’in dan sanda cin hanci.

Amal Umar, Jarumar fina-finan Kannywood a arewacin Najeriya
Amal Umar, Jarumar fina-finan Kannywood a arewacin Najeriya © Daily Nigerian
Talla

Ana zargin jarumar da yunkurin bayar da cin hancin Naira 250,000 ga wani dan sanda, mai suna ASP Salisu Bujama, da ke rundunar ’yan sandan, shiyya ta daya da ke Kano.

A cewar mai gabatar da karar, Amal na yunkurin bayar da cin hancin ne, domin hana binciken ’yan sanda kan zargin saurayinta da almundahanar kudi.

Rundunar ta bayyana haka ne a wani taron manema labarai da kakakin ‘yan sandan ta shiyya ta daya da ke Kano, CSP Bashir Muhammad da ya gabatar a ranar Laraba a Kano.

Ya kara da cewa “Wata jarumar ‘yar wasan Hausa wadda aka fi sani da Amal Umar mai shekara 24 an gurfanar da ita a gaban kotu domin yunkurin bayar da cin hanci da ta yi ga ASP Salisu Bujama wanda yake bincike kan wani batu na damfara da saurayinta ya yi wa wani Alhaji Yusuf Adamu na Naira miliyan 40.”

Wannan na zuwa ne, bayan da wani Yusuf Adamu ta hannun lauyansa ya shigar da korafi ga mataimakin Babban Sufeton Umar Mohammad Sanda, inda yake zargin saurayin jarumar da yin sama da fadi da kudin da ya kai Naira miliyan 40 da sunan kasuwanci.

Ƙorafin da aka shigar ya sa ’yan sanda gudanar da bincike, inda suka gano cewa saurayin jarumar ya tura mata Naira miliyan 13 zuwa asusun ajiyar bankinta.

A cewar kakakin rundunar shiyya ta daya, CSP Bashir Muhammed, an gayyaci jarumar domin amsa tambayoyi daga bisani kuma aka bayar da belinta sai dai an hana ta fita daga wata mota da ake zargin saurayin nata ne ya siya.

Jarumar ta tabbatar cewa kudin da ke cikin asusunta mallakin saurayinta ne duk da ta yi ikirarin cewa Naira miliyan takwas kawai ya tura mata.

Bayan da aka bayar da belinta ne kuma ta garzaya babbar kotu, domin neman a dakatar da ’yan sanda daga binciken da suke a kanta.

Kotun ta hana ci gaba da binciken da ’yan sanda ke yi mata, abin da ya bai wa Amal dama ta yunkurin ba da toshiyar baki ga dan sandan da ke bincike a kan lamarin, ASP Salisu Bujama.

Dan sandan ya ki karbar cin hancin, abin da ya sa aka gurfanar da ita a gaban kotun Majistare a ranar Laraba.

Laifin da ake zargin jarumar ta aikata ya saba wa sashe na 118 na dokar final kod, wadda ta haramta bai wa jami’in dan sanda cin hanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.