Isa ga babban shafi

Jihohin Arewacin Najeriya 7 za su kashe naira biliyan 28 a ciyarwar Ramadan

Wasu jihohin arewacin Najeriya 7 sun sanar da ware kudaden da yawansu ya kai naira biliyan 28 da dubu 300 don ciyar da al’ummominsu a lokacin watan Ramadan a wani yunkuri na saukaka wa jama’a matsin rayuwa da tsadar kayayyakin da ake fama da shi a sassan kasar ta yammacin Afrika.

Wajen rabon abincin buda baki na watan Ramadana.
Wajen rabon abincin buda baki na watan Ramadana. AFP - -
Talla

Jihohin kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa sun kunshi Kano da Katsina da Sokoto da Jigawa da Kebbi da Niger da kuma Yobe, wadanda suka gabatar da wani tsarin ciyarwa ga marasa galihu don tallafa musu.

Kusan galibin jihohin a cewar jaridar ba su bayyana ainihin yawan kudaden da za su yi amfani da su wajen aikin ciyarwar ba, sai dai a jumulce, kiyasi na nuna yiwuwar kudaden su kai biliyan 29.

Tuni dai rashin bayyana ainihin yawan kudaden ya haddasa cece-kuce musamman daga malaman addini da ke ganin akwai bukatar bayyana adadin kudin da aka kashe wajen ciyarwar ta Ramadan.

Jihar Katsina ta sanar da ware naira biliyan 10 daga cikin kasafinta don ciyar da marasa galihu wanda ya mayar da ita jiha mafi ware kudade masu yawa don ciyarwar.

A bangare guda, Sokoto ta sanar da ware naira biliyan 6 da miliyan 700 yayin da Kano ta ware naira biliyan 6, kana Jigawa ta ware naira biliyan 2 da dubu 800 da ‘yan kai.

Sauran sun kunshi Kebbi da ta sanar da ware naira biliyan 1 da rabi, kana jihar Niger da naira dubu 976, sannan Yobe da Naira miliyan 178 don ciyarwar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.