Najeriya ta tura sojoji domin ceto dalibai sama da 250 da aka sace a Kuriga
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu a yau Juma'a ya aike da sojoji domin ceto dalibai sama da 250 da wasu 'yan bindiga suka yi awon gaba a makarantar Kuriga da ke jihar Kaduna.
Wallafawa ranar:
Rahotanni na bayyana cewa harin na jihar Kaduna dai shi ne karo na biyu da aka yi garkuwa da jama’a a cikin mako guda a jihar da ta fi kowacce yawan jama’a a nahiyar Afirka, inda wasu gungun ‘yan fashi da makami a kan babura ke kai wa wadanda lamarin ya shafa hari a kauyuka da makarantu da kuma kan manyan tituna domin farautar kudin fansa.
Ma’aikatan kananan hukumomin jihar Kaduna sun tabbatar da harin da aka kai na garkuwa da mutane a makarantar Kuriga a ranar Alhamis, sai dai ba su bayar da alkaluma ba domin a cewarsu har yanzu suna kan tantance yara nawa aka sace.
An harbe akalla mutum guda a yayin harin, kamar yadda mazauna yankin suka tabbatar.
Wani mazaunin garin Muhammad Adam shi ma ya shaida cewa an yi garkuwa da fiye da 280.
Sace jama’a da aka yi a Kaduna da kuma garkuwa da jama’a mako guda da ya gabata daga sansanin mutanen da mayakan jihadi suka raba da muhallansu a arewa maso gabashin Borno, ya kwatanta kalubalen da Tinubu ke fuskanta wanda ya yi alkawarin samar da tsaro a Najeriya.
Satar jama'a guda biyu kuma ya zo ne kusan shekaru goma bayan mayakan Boko Haram sun sace dalibai a makarantar Chibok.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu