Isa ga babban shafi

Matsalolin da za su addabi arewacin Najeriya a 2024

Bankin Duniya ya yi hasashen cewa, mummunar matsalar tsaro da rikice-rikice da kuma tabarbarewar rayuwa za su ci gaba da addabar wasu kananan hukumomi a jihohin Borno da Kaduna da Katsina da Sokoto da Yobe da Zamfara har ma da Adamawa har zuwa watan Mayun shekara mai zuwa. 

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu kenan.
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu kenan. © premiumtimes
Talla

Bankin Duniyar ya lura cewa, tabarbarewar tattalin arziki na hana samun albarkatun gona a wadannan jihohi, lamarin da zai yi illa wajen samar da hatsi a fadin kasar ta Najeriya

A wani sabon rahotonsa kan tsimin abinci, Bankin Duniyar ya yi hasashen cewa, jumullar hatsin da aka samar a  kakar wannan shekarar ta kai tan miliyan 76.5 a kasashen yammaci da tsakiyar Afrika, abin da ke nufin cewa, an samu raguwar kashi biyu idan aka kwatanta da bara.

Rahoton ya ce, ana sa ran  kasashen Chadi da Mali da Nijar da Najeriya za su bada gagarumar  gudunmawa ta fuskantar samun karancin abincin har zuwa watan Mayun badi.

Alkaluman da Cibiyar Bretton Woods ta fitar sun nuna yadda aka samu koma-baya wajen samar da albarkatun gona a bara a kasashen Chadi da Mali da Nijar da Najeriya.

Cibiyar ta ce, wannan karancin abincin na da nasaba da rashin saukar wadataccen ruwan sama da matsalar tsaro wadda ta takaita wa manoma damar zuwa gonakinsu a Chadi da Mali da Nijar, baya ga tabarbarewar tattalin arziki da ta haifar da cikas wajen tanadar kayayyakin noma.

Cibiyar ta kara da cewa, akasarin yankunan na yammacin Afrika za su ci gaba da kasancewa cikin matsalar karancin abinci daga watan Nuwamba zuwa watan Mayun shekara mai kamawa.

Sauran kasashen da za su tsunduma cikin wannan matsalar sun hada da Burkina Faso da Kamaru a cewar rahoton.

Rahoton ya ce, a cikin watan Nuwamba kadai, tsadar kayayyaki a Najeriya ta haura zuwa kashi 28.20, yayin da tsadar abinci ta yi tashin goron-zabi zuwa kashi 32.84 a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.