Isa ga babban shafi

Gwamnonin Arewa sun lashi takobin yi wa 'yan Tudun-Biri adalci

Gwamnonin Arewacin Najeriya 19 sun amince su yi matsin lamba ga hukumomi don ganin an yi wa mutanen Tudun-Biri adalci bayan harin bam da sojojin kasar suka kai musu cikin kuskure a jihar Kaduna.

Wani bangare na taron gwamnonin arewacin Najeriya a wannan Juma'ar a Kaduna
Wani bangare na taron gwamnonin arewacin Najeriya a wannan Juma'ar a Kaduna © Gombe state government
Talla

 

Kazalika gwamnoni sun yi kira da a gudanar da bincike kan lamarin, suna masu fatan wannan tsautsayin ba zai sake faruwa ba a Najeriya.

Shugaban Kungiyar Gwamnoni kuma Gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya ya bayyana haka a wurin kaddamar da taronsu a wannan Juma'ar a jihar Kaduna.

Shugaban Kungiyar Gwamnonin ya bukaci gwamnonin da su yi shiru na tsawon minti guda domin karrama mutanen da suka rasa rayukansu a sanadiyar harin na Tudun-Biri, yana mai cewa, kare rayukan al'umma da dukiyoyinsu, nauyi da ya rataya a wuyen gwamnati.

Ya kuma jinjina wa gwamnatin tarayya kan yadda ta yi gaggawar mayar da martani jim kadan da faruwar lamarin.

Kungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriyar sun bai wa mutanen Tudun-Biri tallafin naira miliyan 180.
Kungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriyar sun bai wa mutanen Tudun-Biri tallafin naira miliyan 180. © Gombe state government

A bangare guda, gwamnonin sun bai wa mutanen na Tudun-Biri tallafin naira miliyan 180.

Gwamnatin tarayya ta yi alkawarin sake gina garin karkashin wani shirinta na Fulako kamar yadda mataimakin shugaban kasar, Kashim Shettima ya bayyana a lokacin da ya ziyarci mutanen da harin ya rutsa da su a asibiti a jihar Kaduna.

Mutane daga ciki da wajen Najeriya sun yi ta kira da a biya mutanen diyyar kudade tare da bayyana fushinsu kan abin da suka kira sakaci da rashin kwarewar jami'an tsaron Najeriya wanda shi ne dalilin kaddamar da harin na kuskure kan mutanen da ke taron Maulidi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.