Isa ga babban shafi

Ana zaman dar-dar a Yola bayan harin 'yan bindiga a hedikwatar 'yan sanda

Rahotanni daga jihar Adawa dake arewacin Najeriya na cewa, wasu ‘yan bindiga sun kai hari hedikwatar ‘yan sandan jihar da sanyin safiyar Laraban nan, lamarin da ya jefa mazauna birnin Yola cikin firgici.

Jami'an tsaron Najeriya yayin aikin sintiri
Jami'an tsaron Najeriya yayin aikin sintiri AP - Sunday Alamba
Talla

Hedikwatar ‘yan sandar na tsakiyar Jimeta ne a karamar hukumar Yola ta Arewa.

Wasu mazauna birnin sun ce sun ji karar harbe-harbe har tsawon akalla mintuna 30.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Jihar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya tabbatar wa jaridar Daily Trust harin, amma ya ce an shawo kan lamarin.

Nguroje ya ce an dakile harin, amma ba a san ko su waye suka kai harin ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.