Najeriya ta ce gargadin Amurka kan 'yan kasarta zai iya haifar da firgici
Gwamnatin Najeriya ta yi Allah wadai da shawar da Amurka ta baiwa ‘yan kasarta da ke a Najeriyan, tana mai cewar irin wadannan shawarar na iya haifar da firgici mara amfani da kuma yin illa ga tattalin arzikinta.
Wallafawa ranar:
A ranar 3 ga wannan watan ne dai, Amurka ta gargadi ‘yan kasarta da ke Najeriya kan barazanar da ake fuskanta a wasu daga cikin otel-otel da kuma biranen kasar.
Toh sai dai a yayin wata zantawa da manema labarai da ministan yada labarai da wayar da kan al’ummar kasar Mohammed Idris ya jagoranta a Abuja, ya ce irin wadannan shawarwari za su maida hannun agogo baya a kokarin da gwamnatinsu ke yi wajen gayyato masu zuba jari cikin kasar.
Ya ce ako yaushe gwamnati na maida hankali wajen kare lafiyar al’umma da kuma bakin da ke ziyartar kasar.
“Mun samar da tsauraran matakan tsaro a matakin tarayya da na jihohi don tabbatar da tsaron masu yawon bude ido da kuma baki na kasashen waje. Wadannan matakan sun hada da tattara bayanan sirri da horas da jami’an tsaro da hadin gwiwa tare da hukumomin tsaron kasashen duniya da sauransu, don samar da tsaro."
Ministan ya kuma tabbatar da kokarin da jami’an tsaro ke yi wajen samar da tsaro a dukkanin fadin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu