Isa ga babban shafi

Karbar haraji daban-daban shine dalilin durkushewar masana'antu a Najeriya-Kwamitin shugaban kasa

Kwamitin shugaban kasa, kan inganta karbar haraji da dokokin kudi ya shawarci gwamnatin  Najeriya da ta zabtare wasu jerin haraji har 190 da ake karba daga hannun talakawan kasar.

Ana ganin manufofin tattalin arzikin da gwamnatin Bola Tinubu ta bijiro da su ka iya lalata harkokin kasuwancin kasar
Ana ganin manufofin tattalin arzikin da gwamnatin Bola Tinubu ta bijiro da su ka iya lalata harkokin kasuwancin kasar REUTERS - TEMILADE ADELAJA
Talla

Wannan dai na zama wata hanya da za’a bi wajen sakarwa masu kamfanonin da masana’antun kasar mara, ta yadda zasu sami damar gudanar da ayyukan su da kuma samun riba cikin sauki.

Ta cikin wani rahoton bayan bincike da kwamitin ya karantawa shugaban kasar Bola Ahmad Tinubu ya zargi jihohi da karbar harajin da ya wuce kima, kuma bisa rashin ka’ida.

Rahoton kwamitin ya ce wannan harajin barkatai da jihohi ke karba, shine ummul’aba’isin tashin farashin kayayyaki, da rashin samun ribar da ta dace da kuma lalacewar darajar naira da sauran matsaloli.

Kwamitin ya buga misali da korafin da kamfanonin sadarwa suka jima suna yi, game da yadda jihohi suka mayar da su saniyar tatsa ta yadda suke karbar jerin haraje-harajen da aka kasa gane masa ma.

Yayin da yake gabatar da korafin kamfanonin sadarwar, shugaban kungiyar su a Najeriya Gbolahan Awonuga ya ce kowanne kamfanin sadarwa ya na biya haraji daban-daban har guda 40 ko sama da haka duk wata, abinda ya ce yana haddasa musu karancin abokan ciniki saboda tsada.

Shugaban kwamitin shugaban kasar Mr. Taiwo Oyedele ya ce kwamitin na shawartar gwamnatin tarayya ta hade haraje-haraje fiye da 200 daban-daban da masu kamfanoni ke biya zuwa 10 kachal.

Kwamitin ya kuma bukaci gwamnatin tarayya ta yi gaggawar mayar da hankalin ta kan fannin tattalin arziki, don shawo kan matsalar hauhawar farashin kayayyaki da kuma lalacewar darajar Naira.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.