Isa ga babban shafi

Najeriya ta yi nasara a kotun Ingila kan rikicinta da kamfanin P&ID

Gwamnatin Najeriya ta yi gagarumar nasara a kotun Ingila wajen sa kotun ta jingine umarnin biyan wani kamfanin kasashen ketare diyyar dala biliyan 11 saboda soke kwangilar da aka ba shi na samar da iskar gas. 

Najeriya ta samu nasara a kotun birnin London kan rikicinta da kamfanin P&ID
Najeriya ta samu nasara a kotun birnin London kan rikicinta da kamfanin P&ID The Guardian
Talla

A shekarar 2010 gwamnatin Najeriya ta bai wa kamfanin P&ID kwangilar shekaru 20 na ginawa tare da sarrafa iskar gas a sansaninsa da ke kudancin kasar, a yunkurin ganin kasar ta ci gajiyar arzikin makamashin da take da shi. 

Daga bisani, Najeriya ta nuna rashin gamsuwarta da aikin kamfanin abin da ya sa ta sanar da soke kwangilar, kuma nan take kamfanin ya ruga kotu a London a shekarar 2017 domin neman a bi masa kadi. 

Kotun da ke birnin London ta bada umarnin cewar Najeriya ta biya kamfanin P&ID dala biliyan 6 da miliyan 600 a matsayin asarar da ya yi na ribar aikin, yayin kudin ruwan da ya yi ta karuwa kuma ya sa adadin kudin da za a biya kamfanin ya tashi zuwa sama da dala biliyan 11, kudin da ya zarce kasafin kudin Najeriya na bangaren kula da lafiyar jama’ar kasar na shekarar 2019. 

Sai dai lauyoyin Najeriya sun ce ba a yi wa kasar adalci ba wajen wancan hukunci, saboda abin da suka kira bata sunan da kamfanin P&ID ya yi da kuma makudan kudaden da ya bayar a matsayin cin hanci ga wasu manyan jami’an gwamnati domin samun kwangilar tare da bai wa lauyoyin gwamnatin Najeriya cin hanci domin karbar wasu muhimman takardu domin gabatarwa kotun. 

Shi dai P&ID ya musanta cewar ya samu kwangilar ce ta hanyar bada cin hanci da kuma musanta bai wa lauyoyin Najeriya cin hanci domin samun takardun bayanai, inda ya zargi hukumomin kasar da rashin iya aiki a matsayin abin da ya haifar da matsalar da aka soke kwangilar da aka ba shi. 

Alkalin kotun Robin Knowles ya jingine hukuncin biyan kamfanin P&ID diyyar dala biliyan 11 tare da bai wa Najeriya damar kalubalantar hukuncin da akayi a baya lokacin gabatar da nashi hukuncin a yau, yayin da ya tabbatar da cewar an samar da wannan kwangilar da ake takaddama akai ne ta haramcaciyar hanyar da ta sabawa manufofin jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.