Isa ga babban shafi

Najeriya ce kan gaba a duniya wajen yawan mutane marasa muhalli

Wani rahoton shekara shekara da ake fitarwa kan lamurran da suka shafi yawan al’ummar duniya, ya nuna cewar a shekarar bana, Najeriya ce kan gaba a nahiyar Afrika dama duniya baki daya, wajen fama da yawan mutanen da basu da muhalli. 

Wani sansanin 'yan gudun hijira.
Wani sansanin 'yan gudun hijira. © Ngala Killian Chimtom
Talla

Wata kididdiga ta nuna cewar yawan ‘yan Najeriya na karuwa ne da a kalla kashi 2.6 kowace shekara, yayin da a gefe guda yawan marasa muhalli ke karuwa a kasar saboda wasu dalilai, ciki har da rashin wadata ko saukin samun gidaje. 

Kididdigar bana ta nuna cewar a halin yanzu kimanin mutane miliyan 24 da kusan rabi ne basu da muhalli a Najeriya, yayin da Pakistan ke biye a matsayi na biyu da adadin mutane miliyan 20, sai Masar ta uku da mutane miliyan 12.  

Kasa ta hudu wajen yawan maraaa muhallli a duniya kuwa ita ce Syria da adadin mutane miliyan 6 da dubu 568, sai Jamhuriyar Congo ta shida da mutane miliyan 5 da dubu 332. 

Sauran kasashen sun kunshi, Bangladesh da yawan mutane miliyan 5 kana Colombia da yawan mutane miliyan 4 da dubu 943 sai Afghanistan da mutane miliyan 4 da dubu 660 kana Philippines da yawan mutane miliyan 4 da dubu 500.

Kasa ta karshe a sahun ‘yan goman farko mafiya yawan mutanen da ke rayuwa ba tare da muhalli ba ita ce Yemen da jumullar mutane miliyan 3 da dubu 858.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.