Isa ga babban shafi

Obi ya gaza gamsar da kotu kan cewa shi ne ya lashe zaben Najeriya

Kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa a Najeriya da ke zaman yanke hukunci kan karar zaben da aka shigar a yau, ta ce dan takarar shugaban kasar karkashin inuwar jam’iyyar Labour Peter Obi ya gaza gamsar da kotun da hujjojji kwarara kan cewa shi ne ya sami kuri’u mafi rinjaye a zaben na bana.

Peter Obi
Peter Obi © Daily Post
Talla

Mai shari’a Haruna Tsammani wanda shi ne ke jagorantar alkalan kotun guda biyar ya ce har yanzu Peter Obi da lauyoyinsa ba su bayar da gamsassun bayanai kan cewa shi ne ya lashe zaben shugaban kasar ba.

Wannan dai na nufin cewa kotun ta jingine karar da Mista Obi ya shigar yana kalubalantar zaben.

Kotun ta ce shaidu 10 da jam’iyyar Labour da Peter Obi suka gabatar mata ba su da kwarin da za ta dogara da su wajen ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben ko kuma ruhse zaben ba.

Baya ga haka kuma alkali Tsammani, ya ce tawagar lauyoyin Peter Obi sun zarce wa’adin kwanaki 21 da kotun ta bayar don mika mata dukannin shaidun da zasu dogara da su a kotun don haka a wajen ta shaidun su ba su cika ba.

Alkali Tsammani ya kuma ci gaba da cewa lauyoyin Peter Obi suna sane da cewa ya kamata su gabatar da bayanan shaidunsu a rubuce hade da shaidar ranstuwa, amma duk da haka suka yi fatali da wannan doka, suka rika mika wa kotun shaidun da ba su cika ka’ida ba.

Har kawo yanzu dai ana ci gaba da zaman yanke hukuncin a kotun da aka fara tun safe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.