Isa ga babban shafi

Gwamnatin Taraba ta musanta zargin barkewar cutar Anthrax

Gwamnatin jihar Taraba da ke Najeriya ta musanta barkewar cutar Anthrax da ake samu jikin dabbobi musamman shanu a jihar.

Har yanzu dai babu wani tabbaci game da barkewar cutar a jihar ta Taraba.
Har yanzu dai babu wani tabbaci game da barkewar cutar a jihar ta Taraba. AFP - MAURO PIMENTEL
Talla

Gwamnatin na mayar da martani ne kan wasu bayanai da kafofin yada labarai a kasar suka fitar, da ke tabbatar da barkewar cutar.

Daraktan hukumar kula da lafiyar dabbobi ta jihar, Shehu Abdullahi ne ya sanar da hakan yana mai cewa wannan labarin zallar jita-jita ne da bashi da tushe ballantana makama.

Dr Abdullahi, ya ce gwamnatin jihar ta samar da hanyoyi da dama da mutane zasu iya sanar da bullar wannan cuta a hukumance idan an ga alamun ta, kuma har yanzu babu koda mutum daya da ya sanar da gwamnati, don haka a wajen gwamnati wannan zargi ne kawai.

Sai dai ya  ce gwamnatin zata fara wata bita da kuma wayar da kan masu kiwon dabbobi a karamar hukumar Yorro kan yadda zasu gane alamun cutar a jikin dabbobin su da kuma yadda zasu sanar da gwamnati cikin sauki.

Cutar Anthrax cuta ce da ke da alaka da kwayar cutar Bacteria da ke yaduwa jikin dabbobi musamman shanu, kuma tana iya yaduwa cikin hanzari a jikin dan adam.

Ranar 14 ga watan Yulin da ya gabata, itace ranar da aka  sanar da samun bullar cutar karon farko a kasar, cikin wata gonar dabbobi a jihar Neja, sai kuma daga bisani aka sami bullar cutar a jihar Legas.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.