Isa ga babban shafi

Tallafi: Manoma a Najeriya sun yi korafi kan mayar da su saniyar ware

Manoma a Najeriya sun koka game da yadda aka mayar da su saniyar ware, a ci gaba da rabon kudaden tallafin da ake baiwa mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a shekarar 2022.

Hukumar Bunkasa Aikin Gona ta Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci kara kaimi wajen noman abinci mai gina jiki
Hukumar Bunkasa Aikin Gona ta Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci kara kaimi wajen noman abinci mai gina jiki Laurent Correau / RFI
Talla

Tun farko dai gwamnatin kasar karkashin ma’aikatar jin kai da takaita afkuwar Ibtila’i ce ta ware naira biliyan 1 da rabi don rabawa wadanda ibtila’in ya shafa, sai dai manoma sun ce basu san ana yi ba.

Sanin kowa ne dai manoma na cikin wadanda suka fi ji a jikin su sakamakon ambaliyar, la’akari da yadda ruwan ya rika wanke musu gonaki da fadin su ya kai hecta dubu 944 da 989.

Bayanai sun ce ambaliyar ta tafi da mafarkin manoma fiye da miliyan daya na samun gagarumar riba a sakamakon yadda amfanin gonar yayi yabanya kafin afkuwar ibtila’in.

Wannan korafi na zuwa ne bayan da hukumar ta NEMA ta yi ikirarin aiki da jami’an rassanta na jihohi wajen rarraba kayan da suka hadar da kudade, kayan abinci da kuma kayan amfanin yau da kullum.

Wannan dai ba shi ne karon farko da manoma suke makamancin wannan korafi a Najeriya ba, inda suke ganin kusan kowanne lokaci ana mayar da su saniyar ware a tsare-tsaren tallafi da gwamnati ke bijirowa da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.