Jihohi da garuruwan da za su fuskanci ambaliya a Najeriya
Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Najeriya NEMA ta zayyana sunayen jihohi 14 da kuma garuruwa 31 da ta ce za su fuskanci ambaliyar ruwa sakamakon mamakon ruwan saman da za a tafka daga ranar 4 zuwa 8 ga watan Yuki da muke ciki.
Wallafawa ranar:
Hukumar ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da babban jami'in tsare-tsarenta reshen jihar Lagos, Mista Ibrahim Farinloye ya sanya wa hannu.
Farinloye ya bukaci masu ruwa da tsaki a wadannan jihohi da su dauki matakan hana samun asarar rayuka da dukiyoyi.
Jihohi da garuruwan da hukumar NEMA ta zayyana su ne kamar haka:
Filato: Langtang da Shendam
Kano: Sumaila da Tudun wada
Sokoto: Shagari da Goronyo da Silame
Delta: Okwe
Kaduna: Kachia
Akwa Ibom: Upenekang
Adamawa: Mubi da Demsa da Song da Mayo-belwa da Jimeta da Yola
Katsina: Katsina da Jibia da Kaita da Bindawa
Kebbi: Wara da Yelwa da Gwandu
Zamfara: Shinkafi da Gummi
Borno : Briyel
Jigawa: Gwaram
Kwara: Jebba
Niger: Mashegu da Kontagora
A bara an samu ibtila'in ambaliyar ruwa da ya yi sanadiyar rushewar gidaje da lalata dukiyoyi har ma da samun salwantar rayuka baya ga harkokin kasuwanci da suka tsaya cak na wani dan lokaci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu