Isa ga babban shafi

DSS ta bankado shirin kai hare-hare a lokacin bikin sallah a Najeiya

Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya DSS, ta ce ta bankado shirin wasu ‘yan ta’adda da ke kokarin kai hare-hare a wuraren ibada da kuma na shakatawa, gabani da kuma lokacin bukukuwan sallah a fadin kasar.

'Yan sandan Najeriya na hukumar tsaron farin kaya ta DSS.
'Yan sandan Najeriya na hukumar tsaron farin kaya ta DSS. AP - Sunday Alamba
Talla

A cikin sanarwar da kakakin hukumar Peter Afunanya ya fitar, ta bukaci al’umma su kara sanya ido da kuma kai rahoton duk wani al’amari da basu aminta da shi ba ga hukumomin tsaro mafi kusa.

Ya ce hukumar za ta ci gaba da hada kai da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da tsaron rayuka da kuma dukiyar al’umma.

Har wayau, sanarwar ta ce a wani aikin hadin gwiwa da suka yi tsakanin su da jami’an sojoji da ‘yan sanda, a jahohin Nasarawa da kuma Kogi a ranar 19 ga wannan watan, sun samu nasarar kama wani mai suna Abubakar Muhammad da ake zargi da safarar makamai.

Ya ce sun samu nasarar gano ababen fashewa 22 da alburusai da kudi naira dubu 31 da dari 5 da kuma mota kirar Golf a wajen wanda ake zargin.

Haka nan a wani aikin na musamman da suka sake gudanarwa a jiya Alhamis, sun kai hari magoyar wani dan ta’adda da ke da hannu wajen fasa gidan yari a yankin karamar hukumar Ofu na jahar Kogi Kabir Bala, kuma an samu nasarar kashe shi a lokacin musayar wutar da suka yi da jami’na tsaro, ina aka gano bindiga kirar AK47 da wasu kirar gida guda shida da alburusai da wayoyin hannu da dai sauran su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.