Isa ga babban shafi

Akpabio ya zama sabon shugaban Majalisar Dattijan Najeriya

Sanata Godswill Akpabio ya zama sabon shugaban majalisar dattijan Najeriya ta 10, bayan zaben da ya gudana a zauren majalisar a yau Talata.

Godswill Akpabio, sabon shugaban majalisar dattijan Najeriya.
Godswill Akpabio, sabon shugaban majalisar dattijan Najeriya. © Twitter/@daily_trust
Talla

Tsohon gwamnan na Akwa Ibom ya lashe zaben ne bayan samunn kuri’u 63, yayin da abokin takararsa tsohon gwamnan Abdulaziz Yari ya samu kuri’u 46.

Bayanai sun ce Sanatoci 107 ne suka gudanar da zaben sabon shugaban na su.

Da sanyin safiyar yau Talata ne dai rahotanni suka bayyana cewar ana shirin amfani da jami’an tsaro wajen hana Hon Ahmed Wase da Sanata Abdulaziz Yari zuwa majalisar, domin tsaya wa takarar shugabancin majalisun dattijjan da kuma ta wakilai, kamar yadda wata majiya a Abuja ta shaida mana.

Wadanda ke kan gaba wajen takarar shugabancin majalisar wakilan Najeriya sun hada da Ahmed Wase tsohon mataimakin kakakin majalisar a lokacin jagorancin Femi Gbajabiamila, da Tajudden Abbas daga Kaduna, wanda rahotanni ke cewar shi ne wanda jam’iyyar APC mai mulki ke son a marawa baya.

Sauran ‘yan takarar sn hada da Sada Soli daga yankin Jibia na jihar Katsina, da Aminu Sani Jaji daga Zamfara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.