'Yan Najeriya na korafi kan tsadar wutar lantarki duk da karancinta
Duk da karin kudin wutar lantarki da gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi a farkon wannan shekarar da sama da kashi 160, don inganta yanayin samar da wutar, al’ummar kasar na korafi kan biyan makudan kudade, alhali kuwa ba sa samun wutar da suke bukata.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Kunna - 03:06
Gwamnnatin Tarayyar Najeriya ta ce matsaloli masu tarin yawa ne suka haddasa karancin wutar lantarki da ake fuskanta a duk fadin kasar.
To sai dai ministan makamashi na kasar Abubakar Aliyu wanda ya sanar da hakan, ya ce yanzu haka gwamnati na iya kokarinta domin shawo kan lamarin.
Shiga alamar sauti domin sauraron rahoton Khamis Saleh.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu