Isa ga babban shafi

Kotun Najeriya ta hana NBC cin tarar kafafen yada labarai

A Najeriya, wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta ba da umarnin dakatar da Hukumar kula da Harkokin Yada Labarai ta kasa (NBC) daga cin taran kafafen yada labaran kasar.

A Najeriya, wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta ba da umarnin dakatar da hukumar kula da harkokin yada labarai ta kasa (NBC) daga cin taran kafafen yada labaran kasar.
A Najeriya, wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta ba da umarnin dakatar da hukumar kula da harkokin yada labarai ta kasa (NBC) daga cin taran kafafen yada labaran kasar. REUTERS - AFOLABI SOTUNDE
Talla

Yayin sanar da hukuncin ranar Laraba Mai shari’a James Omotosho, ya kuma jingine tarar Naira dubu 500 da hukumar da daura kan wasu kafofin yada labarai 45 a ranar 1 ga Maris na shekarar 2019.

NBC bata da hurumi

Mai shari’a Omotosho ya ce hukumar NBC ba kotun shari’a ba ce, don haka ba ta da wani hurumi na daukar matakan ladaftarwa ko hukunci kan kafafen yada labarai a kasar.

Yace, dokar NBC da ta bata damar daukar mataki kan kafofin ya ci karo kai tsaye da sashe na 6 na kundin tsarin mulkin Najeriya wanda ya daura alhaki yanke hukunci ga kotuna kadai.

Alkalin Ya ce kotu ba za ta zauna a banza tana kallon hukumar ta na cin tara ba bisa ka’ida ba tare da bin doka ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.